Posts

Gawunane gwamnan kano

Image
  Kotun sauraron ƙarar zaɓen gwamnan Kano ta soke nasarar Abba Kabir Yusuf, a matsayin halastaccen gwamna. Haka zalika, ta ayyana ɗan takarar jam'iyyar APC, Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin wanda ya ci zaɓen da ya gudana a ranar 18 ga watan Maris ɗin 2023. Jam'iyyar APC ce ta shigar da ƙara a gaban kotun, tana ƙalubalantar nasarar Abba Kabir. Kotun ta bayyana wannan hukunci na ranar Laraba ne, ta hanyar manhajar Zoom, cikin wani tsattsauran yanayin matakin tsaro a birnin Kano. Mai shari'a Oluyemi Akintan-Osadebay, ita ce shugabar kotun wadda ta jagoranci alƙalan kotun guda uku. Kotun ta ce ta yanke wannan hukunci ne bisa hujjar cewa an yi aringizon ƙuri'u har 165,633, waɗanda aka gano ba su da sitamfi da kuma kwanan wata. Tun farko a watan Maris ɗin 2023, hukumar zaɓen ta ce ɗan takarar NNPP, Abba Kabir Yusuf ya ci zaɓen ne da ratar ƙuri'a 128,900. Abba Kabir Yusuf, in ji INEC ya samu ƙuri'u mafi rinjaye da suka kai 1,019,602, inda Nasiru Yusuf Gawuna da ke biye d...

Arsenal sun dauko Aron Mai tsaron raga

Image
Arsenal ta dauki aron David Raya mai tsaron ragar Brentford kan yarjejeniyar zuwa karshen kakar bana. An kuma bai wa Gunners zabin sayen dan kwallon idan ya taka rawar gani da take bukata. Raya, mai shekara 27, wanda zai sa riga mai lamba 22 zai kalubalanci Aaron Ramsdale a gurbin mai tsaron ragar Arsenal. Ya buga karawa 11 ba tare da kwallo ya shiga ragarsa ba a kakar da ta wuce, wadda Brentford ta kare a na Tara 9 a teburin Premier League.  

Kasar rasha ta gargadi kasashen yammacin Africa

Image
  Ƙasar Rasha ta gargaɗi ƙungiyar Ecowas game da ɗaukar matakin soji da ta ce za ta yi kan sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar. Tana mai cewa matakin ka iya haifar da rikicin da zai daɗe ba a ga ƙarshensa ba. Cikin wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta fitar ranar Juma'a ta gargaɗi ƙasashen yammacin Afirka da kada su aika sojoji zuwa Nijar. Sanarwar ta ce ''Mun yi imanin cewa matakin soji ba zai warware matsalar Nijar ba, a maimakon haka lamarin zai haifar da mummunan rikici, wanda ba a san ranar ƙarewarsa ba, tare da sake dagula lamura a yankin Sahel''. Manyan hafsoshin tsaron ƙasashen Ecowas na shirin wata ganawa a ranar Asabar domin tsara yadda za a shirya dakarun sojin.

Bazoum ya nemi taimakon kasashen duniya

Image
 Tsohon shugaban kasan nijer Bazoum Muhammad ya nemi taimakon kasashen duniya, domin sukawowa kasar agaji domin mayar da ita kan Tafarkin demokaradiyya, Kasar nijer tashiga cikin wani hali na barazana a yayinda wasu daga cikin yan kasar suke goyon bayan mulkin soja,wasu kuma suke nuna rashin jindadinsu,