Arsenal sun dauko Aron Mai tsaron raga
Arsenal ta dauki aron David Raya mai tsaron ragar Brentford kan yarjejeniyar zuwa karshen kakar bana.
An kuma bai wa Gunners zabin sayen dan kwallon idan ya taka rawar gani da take bukata.
Raya, mai shekara 27, wanda zai sa riga mai lamba 22 zai kalubalanci Aaron Ramsdale a gurbin mai tsaron ragar Arsenal.
Ya buga karawa 11 ba tare da kwallo ya shiga ragarsa ba a kakar da ta wuce, wadda Brentford ta kare a na Tara 9 a teburin Premier League.

Comments
Post a Comment