Posts

Showing posts from August, 2023

Arsenal sun dauko Aron Mai tsaron raga

Image
Arsenal ta dauki aron David Raya mai tsaron ragar Brentford kan yarjejeniyar zuwa karshen kakar bana. An kuma bai wa Gunners zabin sayen dan kwallon idan ya taka rawar gani da take bukata. Raya, mai shekara 27, wanda zai sa riga mai lamba 22 zai kalubalanci Aaron Ramsdale a gurbin mai tsaron ragar Arsenal. Ya buga karawa 11 ba tare da kwallo ya shiga ragarsa ba a kakar da ta wuce, wadda Brentford ta kare a na Tara 9 a teburin Premier League.  

Kasar rasha ta gargadi kasashen yammacin Africa

Image
  Ƙasar Rasha ta gargaɗi ƙungiyar Ecowas game da ɗaukar matakin soji da ta ce za ta yi kan sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar. Tana mai cewa matakin ka iya haifar da rikicin da zai daɗe ba a ga ƙarshensa ba. Cikin wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta fitar ranar Juma'a ta gargaɗi ƙasashen yammacin Afirka da kada su aika sojoji zuwa Nijar. Sanarwar ta ce ''Mun yi imanin cewa matakin soji ba zai warware matsalar Nijar ba, a maimakon haka lamarin zai haifar da mummunan rikici, wanda ba a san ranar ƙarewarsa ba, tare da sake dagula lamura a yankin Sahel''. Manyan hafsoshin tsaron ƙasashen Ecowas na shirin wata ganawa a ranar Asabar domin tsara yadda za a shirya dakarun sojin.

Bazoum ya nemi taimakon kasashen duniya

Image
 Tsohon shugaban kasan nijer Bazoum Muhammad ya nemi taimakon kasashen duniya, domin sukawowa kasar agaji domin mayar da ita kan Tafarkin demokaradiyya, Kasar nijer tashiga cikin wani hali na barazana a yayinda wasu daga cikin yan kasar suke goyon bayan mulkin soja,wasu kuma suke nuna rashin jindadinsu,